Akalla mutane 60 ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a wata mahakar zinari a kasar Burkina Faso

0 101

Akalla mutane 60 ne suka mutu jiya sakamakon fashewar wani abu a wata mahakar zinari ta wucin gadi a wani kauye kusa da birnin Gaoua dake kudu maso yammacin Burkina Faso.

Wasu karin mutane da dama kuma sun jikkata ciki har da mata da kananan yara

Jami’an yankin da shaidun gani da ido sun ce fashewar ta faru ne a yayin da wasu abubuwan fashewa da aka ajiye a kusa da wurin da ake hada zinari suka tashi.

An kwashe yawancin mutanen da suka jikkata zuwa asibitin yankin Gaoua.

Wani mai gabatar da kara na yankin da ya ziyarci wurin ya ce an kaddamar da bincike kan lamarin.

Hatsari na faruwa akai-akai a guraren hakar ma’adinan da ke aiki ba tare da izini ba a wasu kasashen Afirka, tare da karancin ka’idojin aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: