Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanya hannu akan kudirin dokar zabe da aka yiwa gyara

0 63

Mai bawa shugaban kasa shawara akan kafafen yada labarai, Femi Adesina, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanya hannu akan kudirin dokar zabe da aka yiwa gyara.

Femi Adesina ya sanar da haka a yau lokacin da ake fira da shi a gidan talabijin na Channels.

Kakakin na shugaban kasa lokacin da yake kare ubangidansa, ya soki wadanda ke zargin shugaba buhari da jinkiri wajen sanya hannu akan kudirin.

Yace jinkirin na shugaban kasa har yanzu yana bisa turbar tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Tunda farko shugaban kasar, ya ki amincewa ya sanya hannu akan kudirin dokar zaben na shekarar 2021 da aka aika masa a ranar 19 ga watan Nuwamban bara, domin bawa jam’iyyun siyasa damar zaben ‘yan takar-karun zabe ta hanyoyi daban-daban.

Majalisun kasa sun gyara hakan kuma sun sake aikawa shugaban kasa kudirin dokar domin ya sanya hannu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: