Domin ceto demokradiyyar Najeriya na kirkira sabuwar tafiyar The National Movement – Kwankwaso

0 88

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, a yau ya sanar da kafa wata tafiya mai suna The National Movement, domin ceto demokradiyyar kasarnan.

Sauran mutanen dake cikin tafiyar akwai tsaffin gwamnoni da na jihar Kogi, Idris Wada, Jigawa Ibrahim Saminu Turaki; Edo, Lucky Igbinedion; Kebbi, Adamu Aliero; da Cross Rivers, Liyel Imoke.

Sauran sune Sanata Suleiman Hunkuyi na jihar Kaduna, tsohon ministan matasa da cigaban wasanni Solomon Dalung da Buba Galadima.

Sauran mashahuran ‘yan Najeriyar dake wajen taron sun hada da dattijo Tanko Yakasai; Mallam Aminu Ibrahim Ringim, Sanata Ubali Shittu; Air Vice Marshall Ifeanaju; Solomon Edoda; Nweze Onu; Falasade Aliyu; Rufai Alkali; Suleiman Hunkuyi; Grace Ben; Ali Gwaska; Paul Okala; Rufai Hanga; Idris Wada; Abdulrahman Abubakar, da sauran mutane dayawa.

Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya hada tafiyar, Rabi’u Musa Kwankwaso yace an samar da tafiyar ne bisa bukatar ceton kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: