Akwai bukatar a mayar da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya tsarin dimokuradiyya

0 97

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya ce akwai bukatar a mayar da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya tsarin dimokuradiyya, yana mai cewa Najeriya da yawan al’ummarta, girman tattalin arzikinta da kuma rawar da take takawa a Afirka tana da ‘yancin zama wani bangare na kwamatin.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wani taron mai taken Tabbatar da Duniyar da ba ta da tsaro, a cewar Alkasim Abdulkadir mai taimakawa Ministan kan harkokin yada labarai a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau.

Ministan yayi jawabin hakan ne yayin ganawa da Sakataren NATO, Jens Stoltenberg; Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan Al Saud; Ministar harkokin wajen Finland, Elina Valtonen; Sanata daga Delaware Amurka, Christopher A. Coons; da Shugaban, kungiyar tattalin arzikin duniya, Børge Brende; da Ministar Harkokin Wajen Tarayyar Jamus, Annalena Baerbock.

An gudanar da taron ne a birnin Davos na kasar Switzerland, a gefen taron tattalin arzikin duniya da aka kammala. Mahalarta taron sun tattauna kan rikice-rikicen da ake ci gaba da yi, da kara tabarbarewar sauyin yanayi, tattalin arzikin duniya mai rauni da kuma hadarin sabbin fasahohin da ke haifar da sarkakiyar yanayin tsaro a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: