Kwamatin tsare-tsare kan tattalin arziki na babban bankin kasa CBN zasu gudanar da taro

0 94

Babban bankin kasa CBN yace kwamatin tsare-tsarensa kan tattalin arziki zasu gudanar da taro karo na farko karkashin jagorancin gwamnan babban bankin Olayemi Cardoso a ranakun litinin da Talata 26 da 27 ga watan gobe.

Sanarwar taron ta biyo bayan wani samun tattauna na kwanaki 2 kan shirye-shiryen zaman ganawar kwamatin na watan Fabareru.

Da yake tabbatar da hakan a Abuja, mukaddashin daraktan sashen sadarwa na bankin Misis Hakama Sidi Ali tace zaman zai tattauna batutuwan da suka shafi zuzzurfan tunani kan manufofin kwamatin.

Ta bayyana cewa, muhimman abubuwan da za’a mayar da hankali a kai yayin zaman, sun hada da tattaunawa kan tsare-tsare don aiwatar da gyare-gyaren da suka dace a tsarin manufofin kudi. Shugaba Bola Tinubu ya nada Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin na CBN a watan Oktoban shekarar da ta gabata, domin ya maye gurbin Godwin Emefiele.

Leave a Reply

%d bloggers like this: