Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce babu shakka za a sake nazari kan dokar da ta kafa sabbin masarautu a Kano.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a jihar ta Kano, Kwankwaso wanda ake wa kallon shi ne uba a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, ya ce an kafa masarautun ne da wata niyya ta daban wadda ba ta dace ba.
Wannan dai wata dambarwa ce da ake yi wa kallon tana ƙasa tana dabo tun ba yanzu ba.
Tun bayan nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu, a matsayin gwamnan jihar Kano a zaben da aka yi a bara, wasu magoya bayansa suka riƙa kiran a rusa masarautun.
Cikin tattaunawar da aka yi da shi ta kimanin sa’o’i biyu, Kwankwaso ya tabo lamura da dama, waɗanda suka hada da batun alaƙarsa da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Sai dai maganar gyaran dokar masarautun jihar ce ta fi ɗaukar hankalin mutanen jahar da ma makwabtanta. A watan Maris ɗin shekarar 2020 ne, gwamnatin jihar Kano ta bakin sakataren gwamnati, Alhaji Usman Alhaji, ta sanar da cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga kujerarsa.