Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da Naira miliyan dubu 5 kan inganta harkokin samar da ruwan sha

0 51

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da naira miliyan dubu 5 domin sayen man disel da sauran kayyayaki domin inganta harkokin samar da ruwan sha a fadin jihar.

Kwamashinan yada labarai, matasa, wasanni, da cigaban al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmad ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a karshen zaman majalisar zartaswa na jiha a Dutse.

Yace majalisar yayin zamanta, ta amince da kudaden a ranar Alhamis domin bunkasa shirin samar da ruwan sha daga watan Junairun nan zuwa watan Decembar karshen shekarar nan. Haka kuma, Gwamna Mallam Umar Namadi ya sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin jiha da wata hakumar bunkasa ayyukan gona ta Turai, domin samar da ingantaccen iri, da kuma bunkasa aikin noman rani tare da horas da manoma a fannoni da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: