An biya yan Fansho kudi Naira miliyan dubu daya da miliyan dari takwas da ashirin da uku a jihar Jigawa

0 73

Asusun Adashen Gata na Fansho na jiha da kuma kananan hukumomin jihar Jigawa ya biya kudi naira miliyan dubu daya da miliyan dari takwas da ashirin da uku a matsayin hakkokin ma’aikata 702 da suka yi ritaya daga aiki a tsakanin shekara ta 2023 zuwa watan Janairu na 2024.

Sakataren zartarwa na Asusun, Alhaji Kamilu Aliyu Musa, ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi ga wadanda za a biya hakkokinsu a pension house.

Yace an biya hakkokin ma’aikatan zuwa rukuni hudu da suka hadar da ma’aikatan da suka yi ritaya daga aiki su 577 da aka biya hakkokinsu har naira miliyan dubu daya da miliyan dari biyar da shida, sai kuma hakkokin ma’aikatan da suka rasu a bakin aiki su 86 da aka biya magadansu hakkokinsu har naira miliyan dari biyu da casein da biyu.

Sauran hakkokin da aka biya sun hadar da yan fansho 38 da suka rasu alhali basu cika shekaru biyar suna karbar fanshon ba aka biya magadansu cikon kudaden fanshon har naira miliyan ashirin da uku da dubu dari takwas da talatin da takwas. Alhaji Kamilu Aliyu Musa ya gargadi ma’aikatan da suka karbi hakkokin nasu dasu guji shiga hannun yan danfara domin kuwa asusun ba ya karbar ko sisi a hannun wani da sunan na goro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: