Alkalan Najeriya na cigaba da jagorantar shari’ar rikicin siyasa a kowace rana

0 358

Babban alkalin alkalan kasa mai sharia Olukayode Ariwoola ya bayyana damuwa kan karuwa rikicin siyasa, da alkalai ke cigaba da jagoranta a kowace rana.

Mai shari’a Ariwoola ya bayyana haka ne jiya yayin rantsar da sabbin alkalan kotunan daukaka kara da aka nada a baya-bayan nan a Abuja.

Babban alkalin ya kuma bayar da shawarar rage yawan shari’o’in da kuma mai da hankali kan wasu hanyoyin warware takaddama wadanda a cewarsa za su rage yawan ayyukan alkalai da kuma adana muhimman albarkatu.

Iyalai da abokanan sabbin alkalan kotun daukaka kara tara sun hallara a kotun kolin, tare da shugabannin kotuna, da shugaban kotun daukaka kara, mambobin Lauyoyin waje da na ciki da sauran manyan jami’an gwamnati.

Babban alkalin ya shawarci malaman masu shari’ar da su kiyaye mutuncinsu da gujewa fitintinu da ka iya kaiwa ga tashin hankali. Biyo bayan umarnin da kotun daukaka kara ta yi, wanda ya baiwa kotun daukaka kara damar samun alkalai 90, rantsar da alkalai tara ya kawo adadin alkalan daga 71 zuwa 80.

Leave a Reply

%d bloggers like this: