Bara Aka Hana Ba Karatun Al’Ƙurani ba – Aliyu Tilde

0 162
Almajrai

Shahararren malamin nan Dakta Aliyu Tilda ya bayyana cewa haryanzu mutane basu fahimci me ake nufi da Almajiranci ba, inda ya ce Ƙoƙarin da gwamnonin Arewa ke yi na hana baran yara da sunan almajirci da alama bai yi wa masu ci da hakkin wadannan yaran dadi ba. Akwai kuma ƴan siyasa waɗanda don ba sa kan mulki za su yi ƙoƙarin kushe duk abinda gomnati maimulki take yi, da yin alƙawuran ƙarya don su cuci talaka, su hau mulki su yi ta sata da cin amana.

Tun da aka fara zancen nan, ba wanda ya fito fili ya ce yana goyon bayan bara don ya san za a bishi da Allah tsine. Amma sai dai a kewaya a jawo Ƙur’ani a jefa shi cikin lamarin don ɓata suna wato a turance (blackmail) da samun goyon bayan sauran mutane, a ce ana son a hana karatun Ƙur’ani alhali ga wasu manyan laifika ba, ahanaba Kamar karuwanci, zinace zinace da dai sauransu.

Sannan ya kara da cewa maganar gaskiya ita ce illar da ake yi wa yara da yawa ta hanyar saka su bara ake ƙoƙarin hanawa da kuma taimaka musu wajan yin karatun zamani kamar yadda ƴaƴan masu hannu da malamai keyi, Su zauna a gaban iyayensu su yi karatun allo, su yi na zamani, su tarbiyyantu da tarbiyyar gidajensu, a gaban iyayensu tunda yanzu karatun Ƙur’anin yanzu ana samunsa a ko’ina ba sai an je wani gari ba.

Dr. Aliyu Tilde

Idan yaro ya balaga, yana da yancin kansa, ya ga zai je tsangayar wani malami don yayi karatu kowane iri ne, watau ya zama almajiri na hakika, wannan babu damuwa. Sai dai a taya shi ma da addu’a saboda kyakkyawar niyya. Ko kasar Sin wato China ya je zabinsa ne. Sai ya ci gaba da koyon Ƙur’ani, har ya rubuta shi iya bakin gwargwadonsa.
Saboda a lokacin zai zama dole yana da sana’a, ba bara zai yi ba, kuma shi baligi ne, ba yaro ba.

Amma yana dan shekara uku zuwa goma, a tilasta shi rabuwa da mahaifiyarsa, zuwa wani waje ya yi rayuwar da take cikin matukar takura a wannan zamanin da take haƙƙi a matsayin karatu ba abinda da za a goyawa baya ba ne in dai hukuma za ta iya tsai da doka.

Su kuma gomnoni sai su tashi tsaye wajen tabbatar da abinda suka ce za su aiwatar da shi. Wasunsu da gaske suke yi; amma wasu sun raba ƙafa; wasu kuma don siyasa sun fito sun nuna ba sa tare da ƴan’uwansu sauran gomnonin arewa a wannan maganar.

Aliyu ya kara da cewa babu yadda al’umma za ta canza muddin bata canza dabi’unta ba. Wurin ƙoƙarin canza ta kuwa, dole masu amfana da tsohon tsari za su soki sabon tsarin ta kowane hali. Amma jama’a sai su duba,su bambamce tsakanin karya da gaskiya.

Dakta ” Mu wadanda muke da haƙƙin ba da ilimin zamani – daga malaman makaranta da shugabannin makarantu da na ma’aikatun ilimi, da gomnoni da ma’aikatan ilimi a Gomnatin Tarayya, duk yakamata mu tashi tsaye mu tsai da cin amanar da ake yi a harkar karatun zamani. Kowa ya yi aikinsa bilhaƙƙi ta yadda za a yi sha’awar a zo a koye shi” Bara kuwa bai taɓa zama addini ba.

Sannan ya kara da cewa “Munsha kira da a yi ƙoƙarin gwama karatun arabiyya da na zamani kamar yadda wadansu da ƴaƴan malamai suke yi”
Aliyu yace In an ga dama ana iya ɗaukan tsarin Pakistan inda za a yi wa yara uzurin shiga firamare har sai sun haddace Ƙur’ani, idan suna so, kafin su shiga makarantar zamani inda za su yi karatun-sauri na shekara uku kacal sai su shiga sakandare.

Sannan yace “Ina goyon baya, dari bisa dari, akan matakin zartar da doka a majalisun jihohi da ke hana barar yara da sunan almajirci ko wani abu dabam. Ita hukuma ba ta hana abu da baki bane mafita, dole ne sai ta sa doka, rubutacciya kuma wacce aka wallafa, don ta haka ne kowa zai san doka ta hana kuma za a ladabtar da shi idan ya karya ta”
Inda yace kuskure ne a kira ta “dokar hana almajirci,” amma ana iya ce mata “dokar hana barar yara.” Amma idan ba a zartar da doka ba, to duk zancen hana bara ya zama dukan kura da gwado.

A ƙarshe ya nanata cewa barar yara da sunan almajirci gomnoni ke ƙoƙarin hanawa bawai karatun Al,qur,ani ba. Idan akwai mai goyon bayan barar yara kanana sai ya fito ya faɗa, mu gan shi.
Amma kar a ci da hakkin Ƙur’ani. A daina fakewa da guzuma a harbi karsana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: