Fanni Shari’a Ya Samu Sabon Sauyi A Jigawa

0 88

Hukumar Shari’a ta Jihar Jigawa, ta dakatar da dogon hutun da Alkalai suke zuwa duk shekara, wanda kuma zasu fara tafiya hutun daga 13 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki.

Wannan yana cikin Doka Mai Namba 5 na shekarar 2020 da Babban Alkalin Jiha, kuma shugaban Majalisar Hukumar Shari’a Hon Aminu Sabo Ringim, ya sanyawa hannun.

A cewarsa, matakin ya biyo bayan yadda aka kwashe lokaci mai tsayi Alkalan suna zaman gida, saboda cutar Corona.

Haka kuma ya ce saboda yadda ake da Shari’oi da yawa da suke jiran a yanke musu hukunci, ya zama dole a dakatar da wannan Hutun saboda a samu rage Cunkoso a gidajen Yari.

Kazalika, ya ce Dakatar da Dokar, yana cikin kundin tsarin Mulkin Kasa na shekarar 1999, wanda aka yi masa Kwaskwarima.

Leave a Reply

%d bloggers like this: