Cacar baka tsakanin Ministan Buhari da Majalisa na sake Daukar Zafi

0 74

Majalissar kasar nan ta sake maidawa karamin ministan kwadago, ayyuka  da aikin yi Mr Festus Keyamo martani, inda ta bayyana cewa ministan bai’san banbancin dake tsakanin kishin kasa da shugabanci ba.

Kafin hakan dai an bayyana cewa a ranar talata data gabata ne ministan yaki ya nemi afuwar majalissar saboda ya daga musu murya  a zuwansa majalissar domin yin bayani kan shirin Gwamnatin tarayya  na daukar mutane Dubu 774 a wani sabon tsarin da take kokarin farawa a fadin kasar nan.

Inda daga bisani a ranar larabar data gabata majalissar ta bayyana kin amincewarta da tsarin saboda rashin yi musu cikakken bayani.

Yayin zantawa da manena labarai a jiya Juma’a shugaban kwamitin yada labarai na majalissar Mr Benjamin Kalu, ya bayyana cewa majalissar ta fiskanci cewa majallisar zartarwar na kokarin nuna musu cewa basu san aikin su ba.

Festus Keyamo, SAN a Majalisa

Sannan ya kara da cewa samun Baraka tsakanin turakunan Gwamnatin guda 3 zai iya haifar da koma bawa wajan ci gaban al’umma. Sannan ya kara da cewa fahimtar junansu zai taimakawa kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: