An Bayyana Sawaba FM a Matsayin abar Kwatance

0 173

An bayyana gidan Rediyon Sawaba a matsayin gidan rediyon jama’a wacce bata nuna kabilanci kuma shirin gidan rediyon mai suna ‘Igbo Kwenu’ shine irinsa na farko a yankin.

Shugaban Kungiyar ‘Yan Kabilar Igbo mazauna Hadejia, Mr. Nicholas Oga ne yayi wannan kiran yayinda ya jagoranci tawagar yan kungiyar zuwa Sawaba FM domin sada zumunci.

Daga nan ne shugaban kungiyar ya bayyana godiyarsa a madadin sauran kabilar Igbo na garin Hadejia bisa ga shirin da Gidan Radiyon yake gabatarwa da harshen nasu mai taken NZUKO Ndi Igbo, a don haka ne ya ce zasu yi hadin gwuiwa da gidan Radiyon a wajen daukar nauyin shirin da kuma tallata kayansu a kafar yada labaran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: