An biya fiye da Naira Miliyan 537 ga daliban jihar Jigawa dake karatu a manyan makarantu 23

0 174

Hukumar bada tallafin karatu ta jihar Jigawa ta ce ta biya tallafin karatu na fiye da naira miliyan 537 ga daliban jiha dake karatu a manyan makarantu 23 dake jihohin Jigawa da kuma Kano

Sakataren Zartaswa na hukumar, Alhaji Saidu Magaji ya sanar da hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai.

Yace an biya tallafin karatu ga dalibai dubu ashirin da dari tara da casa’in da bakwai dake karatu a manyan makarantun jihar Jigawa takwas da kuma manyan makarantun jihar Kano guda 15.

Alhaji Sa’idu Magaji ya kara da cewar suma dalibai mata dake karatu a manyan makarantu an biya musu kudadensu na makaranta kasancewar Ilmin ya’ya mata kyauta ne a Jigawa.

Yace akwai daliban jihar Jigawa su 5,838 dake karatu a manyan makarantun dake wajen jiha da suka hadar jamiar Usman Danfodio Sokoto da Jamiar Abubakar Tafawa Balewa da Jamiar Ahmadu Bello Zaria suma za a tura musu kudadensu na tallafin karatu fiye da naira miliyan 237. Alhaji Saidu Magaji ya cigaba da cewar gwamnatin jihar Jigawa ta biyawa wasu daliban jihar Jigawa da ke karatu a jamiar Tarayya ta Dutse da kuma Jamiar Bayero kudaden makaranta kimanin naira miliyan dari da sittin da bakwai, da dalibai mata 137 da ke karatun tattalin gida kudaden makaranta a kwalejin Ilmi ta tarayya dake Bichi

Leave a Reply

%d bloggers like this: