Dakarun Soji sunyi nasarar hallaka akalla yan bindiga 43 tare da kama wasu 115 a wani sumame

0 186

Shalkwatar tsaro ta kasa tace dakarun ta sunyi nasarar hallaka akalla yan bindiga 43 tare da kama wasu 115 a sumame daban-daban data kaddamar cikin makon daya gabata.

Daraktan lura hulda da jama’a na ma’aikatar Edward Buba, ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar jiya a Abuja.

Edward Buba yace jami’an tsaro sun dukufa wajen yaki da matsalar tsaro tare da lalata dukkan shirye-shiryen masu yunkurin aikata laifuka.

A cewar sa jami’an rundanar na cigaba da farautar yan bindiga a maboyar su.

Yace kawo yanzu rundunar ta tarwatsa tarew da kama shugabannin kungiyoyin tada kayar baya da dama kare da karya lagon su.

Edward Buba ya kara da cewa sojoji sun kama barayin mai 17, tare da kubutar da mutane 39 da akayi garkuwa dasu a kudu maso kudancin kasar nan. Yace dakarun sunyi nasarar kwato danyen mai na sama da naira miliyan 159 tare da gano makamai da sauran kayayyaki

Leave a Reply

%d bloggers like this: