Harin Kaduna kan masu maulidi abu ne da ba zama lamun ta ba – Tinubu

0 165

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana harin Kaduna kan masu maulidi na baya-bayan nan a matsayin abinda ba za’a lamun ta ba.

A watan decembar 2023, wani harin sojoji ya hallaka sama da mutane 100 tare da raunata da dama a kauyen Tudun Biri dake karamar hakumar Igabi dake jihar Kaduna.

Harin ya jawo tofin ala tsine daga bangarori da dama ciki har da wajen kasa, yayin da rundunar sojoji ta dauki alhakin kai harin tana mai neman afuwa.

Wata guda bayan harin shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana bukatar hadin kai hakumomin tsaro damin magance matsalolin cikin gida.

Da yake jawabi ga shugabannin hafsoshin tsaro da hukumomin leken asiri a gidan gwamnati da ke Birnin tarayya Abuja a ranar juma’ar nan, ya gargade su bisa gazawar sojoji wajen gudanar da aikin su yadda ya kamata. Babban hafsan tsaro janar Christopher Musa, wanda ya bayyana harin na Tudun Biri a matsayin abin takaici, yace ba da gangan aka dauki matakin akan al’umar da yakama a kare ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: