Shugaba Tinubu ya amince da kamfanonin jiragen sama 3 domin jigilar maniyyatan aikin hajji

0 247

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kamfanonin jiragen sama 3 domin jigilar maniyyatan aikin hajjin bana.

Mataimakiyar daraktan hulda da jama’a na hakumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON Fatima Sanda-Usara a wata sanarwa data fitar jiya a Abuja.

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa kamfanonin sun hada Air Peace Ltd., FlyNas da Max Air.

Tace amincewar da kamfanonin da gwamnatin tarayya tayi wani yunkuri ne na tabbatar da nasarar aikin hajjin ga maniyyatan na bana.

Kamfanin Air Peace zai yi jigilar miniyyatan daga jihohin Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kwara, Ondo, Rivers da Birnin tarayya Abuja.

Sanarwar tace kamfanin FlyNas zai dauki mahajjata daga jihohin Borno, Lagos, Osun, Ogun, Niger, Sokoto, Kebbi, Yobe da jihar Zamfara. Kazalika kamfanin Max Air zai yi jigilar maniyyata yan jihohin Bauchi, Benue, Kano, Katsina, Kogi, Nasarawa, Adamawa, Oyo, Taraba, Kaduna, Armed Forces, Gombe, jihar Filato da maniyyatan jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: