Za’a koma makarantu a kasar Zambia bayan shafe makonni 3 suna zaune a gida sakamakon barkewar cutar Kwalara

0 155

Dalibai a fadin kasar Zambia zasu koma makarantu bayan shafe sama da makonni uku suna zaune a gida sakamakon barkewar cutar Kwalara.

Ministan ilimin kasar da farko an tsara daliban makarantun Firamare dana sakandire zasu koma karatu a wannan litinin din mai zuwa, amma aka dage zuwa 29 ga watan Janeru.

A wannan lahadin ne, ma’aikatar lafiya a Zambia tace an samu rahotannin mutane 3,015 da suka kamu da cutar, inda mutane 98 suka mutu a watan oktoba na shekarar data gabata.

Ma’aikatar lafiya tayi gargadin cewa bullar cutar na bazaranar ga kiwon lafiyar kasar.

Ministan ilimi a kasar ya bada umarnin a kara tsawaita rufe makarantun kasar, da tsaftace wurare, samar da isassun sinadaran wanke hannu domin dakile cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: