Gwamnatin mu tayi shirin samar da Tam miliyan biyu na Alkama – Gwamna Namadi

0 244

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi yace gwamnatin sa tayi shirin samar da Tam miliyan biyu na Alkama domin fitarwa zuwa kasashen waje karkashin shirin noman Alkama na kasa da na gwamnatin jiha.

Ya lura cewa Najeriya tana da kasar noma mai yalwa da zata iya noman yawan Alkamar da za`a iya fita da ita zuwa kasashen ketare a karkashin sabon tsarin noman Alkama da nufin zama masu dogaro da kai ta wannan fanni.

Malam Umar Namadi wanda ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala wata ganawar sirri da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a Abuja, yace shugaban kasa ya amince da tsarin tare da samun goyon bayan gwamnatin tarayya domin cimma burin da aka sa a gaba.

Malam Umar Namadi ya shaidawa shugaban kasa wasu daga cikin cigaban da jihar Jigawa ta samu, inda ya yabawa shugaban kasar bisa kebe kadada dubu 40 ga jihar Jigawa domin gudanar da shirin noman Alkama na kasa a bana.

Gwamnan yace shugaban kasa Bola Tinubu ya bashi tabbacin samun tallafin gwamnatin tarayya domin ganin jihar Jigawa ta cimma burin da ta sanya a gaba.

Gwamnatin tarayya ta bullo da shirin noman Alkamar ne a watan Nuwamban shekarar da ta gabata a jihar Jigawa a wani bangare na mara baya ga shirin noman Alkama na kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: