An cafke wani da ake zargin dan daba ne da ya addabi masu tuka keke Napep
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke wani da ake zargin dan daba ne da ya addabi masu tuka keke Napep.
A cewar mai magana da yawun rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, wanda ake zargin Umar Musbahu, daga bayan Garka Quarters a karamar hukumar Daura, an kama shi ne a ranar 16 ga Mayu a Katsina.
Ya ce an kama Musbahu ne da taimakon jama’a a yayin da yake yunkurin yi wa wani mai babur mai kafa uku fashi.
Musbahu ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi, inda ya kuma bayyana sunayen wasu mutane biyu Abdulrahman daga Jibia da Dan Hajiya daga jihar Katsina a matsayin masu taimaka masa.