Bola Tinubu na shirin kara habaka ayyukan tara haraji a kasar nan – Kashim Shettima

0 181

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu na shirin kara habaka ayyukan tara haraji a kasar nan, yayin da ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu wani shiri na kara wa ‘yan kasa karin haraji.

Ya yi wannan jawabi ne a jiya Alhamis a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Cibiyar tattara Haraji ta kasa a fadar Shugaban kasa.

Mataimakin shugaban kasa ya kuma gana da cibiyar hada-hadar hannayen jari inda ya yi kira da a sake yin kwaskwarima ga tsarin saka hannayen jari don jawo hankalin matasa da su yi amfani da damammaki a fannin.

Ya ce kamata ya yi sake dubawa tare da chanza fasali ta yadda za’a karfafa hanyoyin cikin gida don gano masu zagon kasa a fannin kasuwanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: