An dakatar da Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jaridu ta Kasa, NUJ, reshen Jihar Jigawa

0 277

Kwamitin gudanarwa na kungiyar ‘Yan jaridu ta kasa reshen jihar Jigawa, a zaman ganawar da yayi a yau, ya dauki matakin dakatar da shugaban kungiyar na Jiha, Garba Muhammad Bulangu, biyo bayan wasu zarge-zarge da ake masa.
Ciki hadda kin halartar taron majalisar kungiyar tsawon watanni 19 da bata wasu daga cikin kundin tsarin mulkin kungiyar.

Kazalika ana masa zargi da hada baki da tsofaffin shugabannin kungiyar ‘Yan Jaridu mata ta kasa reshen jihar Jigawa wajen karbar kudade daga hannun gwamnati.
Bugu da kari, an samu rahotannin cewa Shugaban kungiyar ya siyar da wasu Injinan Janareto na kungiyar ba tare da sanin hukumomi ba, da tafiyar da harkokin kungiyar ba tare da sanin wasu Mambobi ba.

Sannan kwamitin gudanarwa na kungiyar ya nesanta kan sa da kalaman shugaban kungiyar na zargin gwamnati da yin katsalandan a harkokin zabe.
Saboda haka, kwamitin gudanarwa na kungiyar ya dakatar da Garba Muhammad Bulangu tare da nada Nura Sani Bello a matsayin mukaddashin shugaban kungiyar har sai kwamitin ladabtarwa na kungiyar ya kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: