An fara aikin feshin maganin Sauro a kananan hukumomi 3 da suke jihar Jigawa

0 57

Hukumar Tsaftar Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta ce ta fara aikin feshin maganin Sauro a kananan hukumomi 3 da suke jihar Jigawa.

Kakakin hukumar na jiha Alhaji Zubairu Suleman, shine ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Dutse.

A cewarsa, an fara gudanar da feshin ne tun daga ranar 7 ga watan Agusta a kananan hukumomin Hadejia da Ringim da kuma Babura.

Alhaji Zubairu Suleman, ya ce manufar aiwatar da feshin shine domin a kawar da Sauro, wanda kan Iya yada cutar Maleriya, da sauran cututtuka a muhallai.

Haka kuma ya shawarci mutanen jihar nan, su tabbatar da Al’adar tsaftar muhalli, domin hana kwanciyar ruwa a muhallanmu.

Kazalika, kakakin hukumar ya ce hana kwanciyar ruwa a muhallai zai taimaka wajen yakar cizon sauro, wanda shine yake haifar da cutar Maleria, inda ya shawarci mutane su rika tsaftace muhallansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: