Mutum 816 ne cutar Kwalara ta kasa a Najeriya a cewar NCDC

0 82

A kalla mutane 816, ne cutar Kwalara ta kasa a Najeriya tun bayan samun rahoton bullarta a kasar nan, a cewar cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Kasa wato NCDC.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 31,425 ne suka harbu da cutar a jihohi 22 da suke Najeriya ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

Cibiyar NCDC ta ce daga ranar 1 ga watan Janeru zuwa 1 ga watan Agusta na shekarar nan, kimanin mutane dubu 31,425 ne suka harbu ad cutar Kwalara, yayin da kuma tayi nasarar hallaka mutane 816 a jihohi 22 da suke Najeriya.

Cibiyar ta ce Jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto, Bauchi, and Kano.

Sauran Jihohin sune Kaduna, Plateau, Kebbi, Cross River, Niger, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Kwara, Enugu, Adamawa, Katsina, Borno da kum Abuja.

NCDC ta ce cutar tana yaduwa ne a wuraren da babu tsaftar muhalli, da ruwa mai tsafta da kuma karancin tsaftar abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: