An yankewa wani magidanci hukuncin rataya bayan kashe matarsa a

0 72

Wata babbar kotun jihar Jigawa da ke zamanta a Gumel ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani magidanci mai suna Rabiu Mamman.

Mutumin mazaunin kauyen Medin Labo a karamar hukumar Gagarawa, kotu ta yanke masa wannan hukuncin ne bayan samun sa da laifin kashe matarsa.

Alkalin kotun, Mai Shari’ah Abubakar Mohammed Sambo, ya ce kotu ta tabbatar da wannan hukuncin bayan shaidu da bayanai sun tabbatar cewa Mamman ya kashe matarsa a daji. A cewar sanarwar da kakakin ma’aikatar shari’a ta fitar, Zainab Baba Santali, a shekarar 2016 mutumin ya aikata laifin, lokacin da ya kada matarsa daji sannan ya yi amfani da sanda ya rafka mata a ka, nan take rai ya yi halinsa. Sannan ya haka rami ya binne ta

Leave a Reply

%d bloggers like this: