Gwamna Badaru Abubakar ya bukaci mutanen jihar Jigawa da su gudanar da addu’o’i domin samun sauki kan cutar Kwalara

0 63

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, ya bukaci Al’ummar jihar nan su gudanar da addu’oi domin samun sauki kan cutar Kwalara wanda ta bulla a wasu sassan jihar nan tare da kashe mutane.

Gwamna Badaru Abubakar, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakinsa kan sabbin kafafen Sadarwa, Auwal Danladi Sankara, ya rabawa manema labarai a Dutse.

Manema Labarai sun rawaito cewa gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da cewa kimanin mutane 100 ne cutar Kwalara ta kashe a fadin jihar nan.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta jihar Dr Salisu Mu’azu ya bayyana cewa kimanin mutane dubu 5,000 ne suka harbu da cutar a kananan hukumomi 19 da suke jihar nan.

Gwamna Badaru Abubakar, ya bukaci mutane su rika tsaftace muhallansu, da tsaftar Jiki, a matsayin hanyoyin dakile cutar Kwalara.

Kazalika, ya ce gwamnatin jiha tana yin duk mai yuwuwa domin dakile yaduwar cutar a Jigawa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: