An gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na Hukumar Kwastam ga majalisa

0 261

Shugaban Hukumar hana fasa kwabri ta kasa Kwastam, Adewale Adeniyi, a jiya ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na hukumar ga kwamitin majalisar dattijai mai kula da Hukumar a majalisar dokokin kasa.

Adeniyi, yayin da yake kare kasafin kudin shekarar 2024 na naira biliyan 706.43, ya ce zasu mai da hankali ne kan karfafa ayyukan da ake aiwatarwa, da kara kyautata jin dadin ma’aikata ta hanyar ingantawa da karfafa kwazon jami’an, da kuma samar da fasahohi cikin ayyukan su.

Dangane da jindadin jami’an, Adeniyi ya bayyana cewa za a karfafa gwiwar jami’an ta hanyoyi daban-daban don kara kwazo da inganta jin dadinsu.

Ya ce za a yi hakan ne ta hanyar karrama su, da yi musu karin girma, da kuma biyan alawus-alawus din jami’an. Bugu da kari, shugaban hukumar ta Kwastam ya yi alkawarin cewa zasu kara bunkasa hanyoyin samarda kudaden shiga a shekarar 2024.

Leave a Reply

%d bloggers like this: