Gwamna Umar Namadi ya yi gargadi cewar manoman da aka baiwa bashin kayayyakin noma karkashin shirin noman alkama na kasa kuma basa cikin shirin zasu biya farashin irin yadda yake a kasuwa
Ya yi wannan gargadin ne a lokacin da tawagar bankin raya kasashen afirka ta ziyarci ofishinsa.
Gwamna Mallam Umar Namadi ya kara da cewar tawagar aikin gona ta jiha zata fara rangadin gonaki da aka yiwa rijista karkashin shirin domin gano wadanda aka baiwa kayayyakin aikin noman alkama kuma suka ki nomawa
Gwamnan yana mai cewar suna da bayanan manoman dake cikin shirin noman alkama a jihar nan.
Malam Umar Namadi yace gwamnatin jiha ta yanke shawarar daukar malaman gona masu digiri 400 aiki domin aiwatar da tsare tsaren aikin gona a jihar nan, kasancewar yana daya daga cikin kudirorin gwamnan 12