Majalisa ta gayyaci Nyesom Wike, Nuhu Ribadu, da shugabannin tsaro

0 215

Majalisar wakilai ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan Harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da shugabannin tsaro kan tabarbarewar tsaro a Abuja.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Aguta, daga jihar Anambra, Dominic Okafor ne ya gabatar da kudirin a jiya Laraba.

Ya kuma ce tun lokacin da gwamnatin da ta shude ta fito da tsarin yin rajista, da kuma hada lambar zama dan kasa ta NIN, ba a taba amfani da ita wajen magance matsalar rashin tsaro a babban birnin tarayya Abuja, ko kasar nan ba.

An amince da kudirin ne, a lokacin da Tajudeen Abbas, kakakin majalisar ya ya bayarda umarnin kada kuri’a ta hanyar sautin murya.

Majalisar ta yanke shawarar gayyatar ministan babban birnin tarayya Abuja, da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, da shugabannin dukkanin hukumomin tsaro, domin gudanar da taron gaggawa da kawo dabarun tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: