INEC ta bayar da takardar shaidar cin zabe ga wadanda suka yi nasara a zaben da aka yi ranar Asabar

0 279

A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayar da takardar shaidar cin zabe, ga wadanda suka yi nasara a zaben da aka yi a ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa, an gabatar da takardar shaidar ne a wani biki da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Wadanda suka samu takardar shedar sun hada da Farfesa Anthony Okorie, zababben Sanata mai wakiltar Ebonyi ta Kudu da Pam Dachun, zababben Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa da Musa Mustapha, zababben Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas.

Sauran sun hada da Ifeanyi Ozokwe, mai wakiltar Nnewi ta arewa da Ekwusigo ta kudu da Clara Nnabuife, dan majalisa mai wakiltar Orumba ta arewa da ta kudu, da dai sauransu. Da yake jawabi jim kadan bayan karbar takardar shaidar sa ta ci zabe, Okorie ya sadaukar da nasarar sa ga al’ummar Ebonyi ta Kudu, inda ya bukace su da su yarda da kudirorin sa domin ya zama wakilinsu nagari a majalisar dattawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: