An gano wata gawar wani yaro zabiya da aka sace

0 93

An gano gawar wani yaro zabiya dan shekara hudu kwana daya bayn an sace shi ranar Lahadi a gabashin Burundi

An tsinci gawar Igiraneza Abdoul ne a wani daji.

Yanzu dai an kama mutum uku, wadanda suka hada da ‘yan achaba guda uku, yayin da wani kuma da ake nema da bisa zargin alaka da lamarin ya tsere, amma ana nemansa.

Igiraneza Abdoul na wasa ne da sauran yara abokana a gundumar

Muramvya ta shiyyar Kinama a lokacin da wasu mutane a cikin tasi suka dauke shi.

Mahaifiyarsa Kwizera Marie Godeberte ta gay awa BBC cewa wata motar tasi ce ta zo inda suke, sai kawai duka yaran suka shiga cikinta.

Ta kara da cewa: “Da kusan karfe 7:30 ne na dare. Mun yi nema a ko’ina muka sanarwa a shafukan intanet amma ba labari.”

Kungiyar kare zabiya ta duniya ( Albinos Sans Frontières) ta ce kisan ya tayar mata da hankali, wanda ya a a yanzu yawan wadnda aka kashe a Burundi tun 2008 ya kai 28

Leave a Reply

%d bloggers like this: