Gwamnatin tarayya ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin dawowar zaman lafiya cikin gaggawa

0 107

Gwamnatin tarayya ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin dawowar zaman lafiya cikin gaggawa a duk kauyuka da al’ummomin da ta’addanci ya shafa a fadin kasar.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin Katsina a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar bisa rasuwar mahaifiyar hamshakin attajirin Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da sa ran sauye-sauye da kuma inganta tsarin tsaro a kasar, yana mai cewa gwamnatin tarayya na daukar wasu matakai.

A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yabawa mataimakin shugaban kasar bisa ziyarar da ya bayyana a matsayin mai tarihi da muhimmanci musamman ganin matsalar rashin tsaro ta zama abin damuwa ga mutane da dama.

Sarki Usman ya kuma yabawa Gwamnatin Tarayya bisa yadda ta ayyana ‘yan faahin daji a matsayin ‘yan ta’adda domin jami’an tsaro su yi maganinsu da gaske.

Leave a Reply

%d bloggers like this: