Kimanin Matasa 2,577 ne Hukumar Samar da Ayyukanyi ta Kasa ta bawa Horo kan Sana’oi a jihar Jigawa

0 103

Kimanin Matasa Dubu 2,577 ne Hukumar Samar da Ayyukanyi ta Kasa ta bawa Horo kan Sana’oi Dogaro daban-daban a nan Jihar Jigawa domin dakile Fatara da talauci.

Shugaban Ofishin Hukumar a Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Jamo, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da Manema Labarai a Ofishin su da ke Dutse.

Alhaji Jamo, ya ce Matasan da aka bawa horon sun hada da Maza da Mata, kuma an basu horon ne kan sana’oi daban-daban tun daga watan Janeru zuwa Disambar bara.

Haka kuma ya ce Mutane dubu 1,356 ne Sashen Horas da Sana’oin hannu na hukumar ya bawa dabaru.

Shugaban Ofishin, ya ce Matasa 900 sun samu horo ne kan Kanana da Matsakaitan Kasuwanci a jihar nan.

Kazalika, ya ce wasu Matasan kuma sun samu bashin Naira dubu 100,000 domin su fara kasuwancin su.

A cewarsa, manufar hakan shine domin a rage talauci a matsakanin Matasa da suke Jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: