Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya yabawa dan majalissar wakilai ta kasa Dr Abubakar Hassan Fulata bisa samarwa da alummar mazabarsa kayayyakin bunkasa tattalin arziki.

Gwamnan ya yi wannan yabon ne a lokacin bikin kkaddamar da rabon kayayyakin bunkasa tattalin arziki ga shugabannin jamiyyar APC da kuma sauran magoya baya.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Mataimakin gwamnan jiha Mallam Umar yace rabon kayayyakin na daga cikin kudirin gwamnatin jiha na bunkasa tattalin arzikin jamaar jihar nan.

A jawabinsa mataimakin shugaban majalissar wakilai ta kasa Alhaji Abdullahi Wase ya bayyana Dr Abubakar Fulata dan majalissar wakilai da suke alhafari dashi.

A nasa jawabin Dr Abubakar Hassan Fulata yace wannan shine karo na biyu na rabon kayayyakin bunkasa tattalin arziki da ya gudanar kuma ya gargadi wadanda aka baiwa kayayyakin su guji Sayarwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: