Wata ɗalibar jami’a a Indiya ta gurfanar da makarantar tasu a kotun gundumar Udupi tana neman a ba ta damar saka hijabi a aji.

Ɗan uwan matashiyar mai suna Mubarak Faruk ne ya shigar da ƙarar a madadin ‘yar uwarsa Resham Faruk.

Sun haƙiƙance cewa ra’ayin saka hijabi haƙƙinsu ne da kundin tsarin mulki ya ba su.

Shugaban majalisar amintattu na jami’ar wanda ya gana da masu zanga-zanga kan haramta saka hijabin, ya jaddada cewa ba za a bar ɗaliban da suka saka hijabi suka shiga aji da shi ba.

BBCHausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: