Shugaba Buhari yayi alkawarin jajircewarsa wajen mika mulkin kasarnan bayan ta ginu a aikin gona

0 80

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari jiya a Abuja yayi alkawarin jajircewarsa wajen mika mulkin kasarnan bayan ta ginu a bangaren aikin gona da cigaban tattalin arziki da daidaituwar mulkin demokradiyya da kuma dakarun tsaro masu inganci.

Da yake magana a taron liyafar cin abincin dare da aka shirya domin karrama kwamitin shugabannin siyasa da na kungiyoyin fararen hula da na ‘yan kasuwa da na ‘yan jarida, shugaban kasar yace yana shirin kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2023, inda zai kafa tarihi na mika kasarnan a dunkule mai zaman lafiya, wacce aka gudanar da mulkin demokradiyya na tsawon shekara 24 ba tare da tangarda ba.

Da yake bayyana farincikinsa bisa yadda manyan attajiran Najeriya a yanzu suke hankoron hada kai da ‘yan siyasa domin cigaban Najeriya, shugaba Buhari yayi nuni da cewa samar da matsaya guda akan lamuran da suka shafi tattalin arziki, tsaron kasa da shugabanci da sauran bangarori masu muhimmanci, hanya ce mai kyau da samar da goben da ake bukata.

Dangane da ayyukan kwamitin, shugaban kasar yayi amannar cewa mutanen da suka halarci kaddamar da kwamitin a ranar Lahadi, sun fito daga kowane bangare na al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: