

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Hukumar kula da ayyukan ‘yansanda ta kasa ta koka dangane da yadda ‘yan fashi da makami ke samun damar zuwa sansanonin daukar ‘yansanda.
Shugaban hukumar, Musliu Smith, ya bayyana koken a jiya yayin taron wayar da kai na wuni guda akan aikin daukar sabbin ‘yansanda, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi.
Musliu Smith, a jawabinsa wanda mataimakiyar darakta a hukumar, Hawa Komo, ta karanta, yayi nuni da cewa akwai bukatar duba lamarin.
Yace hakan na nufin ‘yan fashi ne za suke sintiri kan tituna muddin suka zama ‘yansanda.
Shugaban yace manufar taron shine tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da sauraron matsalolinsu da nufin magancesu domin kyautata alaka da ‘yan kasa.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, yace dole a bawa sarakunan gargajiya damar tabbatar da halayya da asalin duk wanda yake neman aikin dansanda daga garuruwan da ke karkashinsu.