Kamfanin NNPC ya kashe biliyan 100 a 2021 wajen gyara matatun mai a Najeriya

0 88

Kamfanin man fetur na Najeriya Nigerian National Petroleum Company (NNPC) ya ce ya kashe naira biliyan 100 kan gyaran matatun mai na ƙasar a cikin shekarar 2021.

NNPC ya bayyana hakan ne cikin wani rahoton shekara da ya gabatar wa asusun haɗaka na gwamnatin tarayya da jihohi yayin wata ganawa, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Duk da cewa ba a bayyana matatun ba, NNPC ya ce ya kashe naira biliyan 8.3 a kowane wata na 2021 don gyara matatun man.

Matatun man da ke ƙarƙashin kulawar NNPC sun haɗa da ta Fatakwal da Kaduna da Warri.

Baki ɗayansu, suna da ƙarfin tace gangar mai 445,000 duk rana, kuma duk da cewa Najeriya na da matatu huɗu, tana kai ɗanyen mai ƙasashen waje a tace sannan ta sayo tataccen don shigowa da shi cikin ƙasar.

BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: