An gargadi ga masu ababen hawa kan rashin bin dokikin fitulun bada hannu

0 137

Hukumar babban birnin tarayya, ta yi gargadi ga masu ababen hawa kan rashin bin dokikin fitulun bada hannu a Abuja.

Daraktan kula da zirga-zirgar ababen hawa na sakatariyar sufuri na Abuja, Mista Wadata Bodinga ne ya yi wannan gargadin a wata hira da manema labarai a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce za a sanya tara mai tsoka ga duk wanda ya karya dokar hanya.

A cewarsa, duk da cewa karya dokokin tuki ya ragu da kashi 80 cikin 100, amma har yanzu ba’a samu yadda ake bukata ba a birnin tarayya Abuja. Bodinga ya kara da cewa, ana ci gaba da inganta fitilun zirga-zirgar ababen hawa domin baiwa na’urorin damar daukar bayanan zirga-zirga a dukkan mahadar da ke cikin birnin, inda ya ce nan ba da dadewa ba za a fara aiki da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: