Dakarun bataliya ta 192, sashe na 81, na rundunar sojojin kasar nan, sun kama wasu da ake zargin manyan dilolin masu safarar miyagun kwayoyi ne a kan iyakar Balogun da ke jihar Ogun.
Sanarwar da Daraktan yada labaran rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, y
a ce sojojin sun gano haramtattun abubuwa guda 296, wadanda ake kyautata Aaron miyagun kwayoyi ne, da aka boye a cikin wata mota kirar Sienna.
Wadanda ake zargin, Adigun Olatunji mai shekaru 54 da kuma Michael Atanda mai shekaru 18, dukkansu ‘yan garin Ilara Imeko a karamar hukumar Afun ta jihar Ogun amma kuma suna zaune a jamhuriyar Benin, an tsare su ne bayan wani yunkurin ba da cin hancin Naira miliyan 12 ga sojoji.
Binciken da sojoji suka gudanar ya nuna cewa an yi safarar haramtattun kayan ne daga jamhuriyar Benin ta cikin kauyukan Ilara dake kan iyaka da zuwa Ifo a jihar Ogun. Nwachukwu, yace masu fataucin kwayoyin, wadanda ke yin safarar daga wata kasa zuwa wata, sun shafe watanni biyar suna shirya yadda zasu shigo da tabar wiwi domin kai wa abokan huldarsu.