An Ginawa Masu Hidimtawa Ƙasa Sabon Masauki A Kazaure

0 160

Gwamnatin jihar Jigawa tayi bikin mika sabon masaukin masu yiwa kasa hidima, NYSC, da ta gina ga Hukumar masu yiwa kasa hidima, a garin Kazaure.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, shine ya mika makullan masaukin masu yiwa kasa hidimar ga babban daraktan hukumar, Birgediya Janar Ibrahim Shu’aibuYace gwamnatin jihar Jigawa ta gina masaukan masu yiwa kasa hidima a kowacce karamar hukuma domin rage matsalolin wuraren kwana ga masu yiwa kasa hidima da ake turowa aiki jihar.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan ilmi, kimiyya da fasaha, Dr Lawan Yunusa Danzomo. Yace Jihar Jigawa ce kan gaba wajen biyan alawus-alawus ga masu yiwa kasa hidima da kuma katafaren sansanin horas da masu yiwa kasa hidima da babu irinsa fadin kasar nan.

A jawabinsa babban daraktan hukumar Janar Ibrahim Shu’aibu yace Jihar Jigawa ce ta farko wajen ginawa masu yiwa kasa hidima masaukai a fadin kasar nan, inda ya yi fatan sauran jihohi zasu yi koyi da ita.

Ya kuma bukaci babban jami’in hukumar na jihar Jigawa, Ibrahim Muhammad, da ya tabbatar da kulawa da gidajen kamar yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: