An girke ma’aikatan agajin gaggawa a sassa daban-daban na birnin Kyiv
An girke ma’aikatan agajin gaggawa a sassa daban-daban na birnin Kyiv inda hare-haren makamai masu Linzami na Rasha ya ɗaiɗaita.
Magajin birnin Kyiv Vitali Klitschko, ya ce hanyar shiga tashar jirgin ƙasa da cibiyar makamashin birnin sun cika maƙil da mutanen da suke neman mafaka.
Jami’an sojin Ukraine sun ce sun kakkaɓo sama da makamai masu linzami 12 da ke cin dogon zango waɗanda Rasha ta harbo kasar.
Ɗaukacin ƙasar dai na zaune cikin shirin ko-ta-kwana, sannan an girke jiragen yaƙi da waɗanda ƙungiyar tsaro ta NATO ta kawo domin tsare sararin samaniyarta.