Gwamnatin sojin Nijar ta bude rajista domin tattarawa tare da adana sunayen wadanda ake zargi a kasar da harkokin ta’addanci, kamar yadda tashar talabijin na kasar RTN Tele Sahel ya ruwaito a jiya.
A wata doka da shugaban sojin kasar Birgediya Janar Abdourahmane Tiani ya sanya wa hannu, ta ce duk wani mutum da ya shiga rajistar, za a kwace kadarorinsa, a hana shi tafiya, sannan za a iya kwace shaidar zama dan kasar Nijar.
matukar an kama mutum da taimakon ta’addanci ko dai shiga ciki ko tsarawa ko kasancewa cikin kungiyar ta’addanci ko aware ko wata kungiya da ke barazana ga zaman lafiyar kasar.
Laifukan da za a duba sun kunshi daukar makami domin yaki da kasar, bayar da bayanan sirri ga kasashen waje, taimakon kasashen waje shigowa kasar da kuma fitar da wasu bayanai ko kalamai da za su iya tayar da zaune tsaye a kasar.
Tun bayan hambarar da Mohamed Bazoum daga mulki ne kasar take fuskantar karuwar harkokin ta’addanci, inda aka fi kai hare-hare a kan sojin kasar, musamman a yankin Tillaberi.A wani labarin kuma, Rahotanni na cewa akalla sojojin Nijar bakwai ne ake zargin ‘yan bindiga sun kashe a ranar 26 ga watan Agusta bayan wani hari. Da ake kyautata zaton mayakan alKaeda ne suka kai a yankin Tillaberi mai fama da rikici a yammacin na Nijar