Kungiyar Afenifere ta yi kira ga gwamnatin tarayya da tashi tsaye don ceto Najeriya

0 101

Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere ta yi kira ga gwamnatin tarayya da tashi tsaye don ceto Najeriya da al’ummarta daga durkushewa gaba daya.

Kungiyar ta bayyana damuwarta game da barnata  dukiyar kasar a yayin da rayuwar al’ummar Najeriyar ke kara tabarbarewar tun bayan hawa mulkin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban kungiyar Oladipo Olaitandan da mataimakin sakatare na kungiyar, Alade Rotimi John suka fitar sun ce ‘halin da ake ciki ya jefa kasar cikin wani yanayi na tsaka mai wuya da rudani’

Kungiyar  ta ce ‘’ Alummar Najeriya na cikin damuwa matuka sakamakon wahalhalun da ake fama da su da yunwa da rashin tsaro da tsaddar rayuwa da rashin aikin yi da kuma hauhawar farashin kayayaki’,’ Kungiyar ta ce wadannan matsaloli sun kara ta’azara halin da alummar kasar ke ciki idan aka kwantata da na baya,

Kungiyar Ta nuna damuwa kan irin rikon sakainar kashi da halin ko in kula da rashin hagen nesa da gwamnati Tinubu ke yi dangane da irin illar da ke tattare da manufofin gwamnati.

Game da haka ne kungiyar ta Afenifere ta yi kashedi kan barnatar dukiyar kasa tana mai cewa: ‘’Dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 240 da aka cire na sayan jirgin shugaban kasa da kuma karin naira miliyan 150 alamari ne da ba za’a amince da shi ba’’

da kuma batun sanya miliyan 950 naira wajen sayan motocin shugaban kasan da kuma naira biliyan 21 da aka ware don yiwa gidan mataimakin shugaban kasar kwaskwarima da fitar da naira biliyan 90 don yin kwaskwarima a gidan shi kansa shugaban kasar sun bayyana hakan da almubazzaranci da dukiyar kasa

Kungiyar ta yi zargin cewa akwai rashin sanin yakamata kan yadda ake barin talakawan kasar cikin kunci da kuma matsalolin tafiyar da alumaran mulkin kasar ba tare da bin kaida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: