An gurfanar da Shugaba Muhammadu Buhari tare da Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed

0 82

An gurfanar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a gaban kotu, kan dokar hana ’yan jarida da gidajen rediyo bayar da rahoto akan hare-haren ta’addanci da wadanda abin ya shafa.

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci dacibiyar fasaha dacigaban ‘yan jarida, wadanda suka shigar da karar sun kuma shigar dahukumar kula da watsa labarai ta kasa cikin wadanda ake kara.

An ruwaito cewa hukumar kula da watsa labarai ta kasa ta nemi ‘yan jarida da gidajen talabijin da na rediyo a Najeriya da su daina bayar da bayanai da yawa kan munanan ayyukan ‘yan ta’adda da masu satar mutane yayin nazarin jaridun da suke yi yau da kullum.

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci dacibiyar fasaha da cigaban ‘yan jaridasun yi ikirarin cewa gazawar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wajen umartar hukumar kula da watsa labarai ta kasa yasa ta janye umarnin da ta bayar game da bayar da labarin hare-haren ta’addanci da wadanda aka ci zarafinsu, ya sabawa sassan kudin tsarin mulkin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: