Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) sun yi barazanar sake tafiya yajin aiki

0 46

Kungiyar Malaman Jami’o’i sun yi barazanar cigaba da yajin aikinda ta dakatar tun a watan Disambar 2020 saboda zargin Gwamnatin Tarayya na kin cika alkawaruka dayawa daga yarjejeniyar da ta sanya hannu tare da kungiyar.

Shugaban kungiyar na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Dr. Ibrahim Inuwa, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da wasu ‘yan jarida a sakateriyar kungiyar.

Ya ce yajin aikin wanda aka shiga domin bukatunsu na dorewar wanzuwar tsarin jami’o’in gwamnati a Najeriya, an dakatar da shi a watan Disamba bayan bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan batutuwa daban-daban da jadawalin aiwatar da dukkaninsu guda 8.

Ibrahim Inuwa, wanda ya ce sama da watanni 7 bayan sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, batutuwa 7 ne kacal daga cikin batutuwa 8 aka samu magancewa.

Ya lissafa wasu daga cikin batutuwan da suka hada da alawus din koyarwa da kudin tallafawa don farfado da jami’o’in gwamnati, da karancin albashi, da yawaitar jami’o’in jihoshida kuma kwamitin ziyartar makarantu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: