Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kalubalen da Najeriya ke fuskanta ba na kabilanci ko addini bane

0 97

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kalubalen da kasarna ke fuskanta ba na kabilanci ko addini bane.

Ministan yace wasu mutane kasarnan na kara dagula kabilanci da bambancin addini don wargaza kasarnan saboda dalilan son kansu.

Lai Mohammed ya yi zanta a Abuja a jiya a wurin bikin gabatar da littafin da cika shekara 75 a duniya na Bamigboye Ogunbiyi, wani sanannen likitan mata.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa Ogunbiyi wanda ya fito daga Ilofa a jihar Kwara shi ne mijin Clara Ogunbiyi, mai shari’ah akotun koli da ta yi ritaya daga jihar Borno.

Da yake gabatar da tarihin rayuwar Ogunbiyi, Ministan ya ce abubuwan da suka hada kan kasarnan sun fi muhimmanci fiye dawadanda ke raba kawunan mutanen kasarnan.

Ya cemagabatan kasarnan tuntuni suka gina tubalin hadin kan kasarnan, kuma abin da mutane ke bukatar yi shi ne tabbatar da dorewarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: