An Kama Kwamandojin Boko Haram da ISWAP da Suka Dawo daga Aikin Hajji A Filin Jirgin Sama Na Katsina
An Kama Kwamandojin Boko Haram Da ISWAP Da Suka Dawo Daga Aikin Hajji A Filin Jirgin Sama Na Katsina
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kama wasu da ake zargin kwamandojin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP su bakwai yayin da suke dawowa daga aikin Hajji a ƙasar Saudiyya ta filin jirgin sama na Katsina.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce an samu nasarar cafke waɗanda ake zargin ne sakamakon inganta tsarin tantance bayanan ‘yan ƙasa da gwamnatin tarayya ta aiwatar, inda daga bisani aka miƙa su ga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS).
Ya bayyana cewa wannan nasara ta nuna yadda sabbin gyare-gyaren da aka yi a tsarin tantance bayanan ‘yan ƙasa da kuma kula da iyakoki ke taimakawa wajen ƙarfafa tsaron cikin gida.
Ministan ya yi wannan bayani ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa ta Ƙasa (NIMC) ta shekarar 2026.
A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta tarar da tsarin bayanan ‘yan ƙasa a rarrabe, inda bayanan hukumomi daban-daban ba sa aiki tare. Sai dai yanzu an haɗa bayanan NIMC da na Hukumar Shige da Fice da sauran hukumomi.
Tunji-Ojo ya ce a halin yanzu ba zai yiwu mutum ya samu fasfo ba tare da an tantance bayanansa daga NIMC ba, kuma tsarin yana aiki tare da bayanan Interpol, lamarin da ya taimaka wajen gano waɗanda ake zargi.
Ya ce, “A makon da ya gabata ne aka kama wasu da aka sani a matsayin kwamandojin Boko Haram da ISWAP guda bakwai lokacin da suke dawowa daga Makkah ta filin jirgin sama na Katsina, sannan aka miƙa su ga DSS.”
Wannan na zuwa ne bayan Dakta Bashir Kurfi ya yi iƙirarin a wani shiri na Trust TV cewa gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki nauyin wasu masu ɗauke da makamai zuwa aikin Hajji.
Sai dai gwamnatin Jihar Katsina ta musanta zargin, inda Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa iƙirarin ba shi da tushe kuma an yi shi ne domin yaudarar jama’a da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin tsaro ke yi wajen yaƙi da rashin tsaro.
Gwamnatin ta ƙara da cewa wasu na siyasantar da batun tsaro domin cimma muradunsu na siyasa da kuma karkatar da hankalin jama’a daga nasarorin da ake samu wajen yaƙi da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.