An kama masu garkuwa da mutane da ƙwato bindiga a Filato
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato ta kama waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane su biyu, tare da samun bindiga nau’in AK-47 maƙare da harsasai guda 30 a Ƙamar Hukumar Kanke.
Hakan na cikin abin da ta kwatanta da wata babbar nasara a yaƙi da aikata laifuka a faɗin jihar.
Waɗanda ake zargin, dukansu ’yan ƙauyen Nyinang ne da ke gundumar Amper a ƙaramar hukumar Kanke, an kama su ne a ranar 2 ga Agusta, 2026, sakamakon wani samame na sirri da aka ƙaddamar biyo bayan rahoton wani lamarin garkuwa da mutane.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Filato, Alfred Alabo ya fitar a ranar Laraba, rundunar ta samu rahoton gaggawa game da garkuwa da mutane a ranar 1 ga Agusta a Ofishin ’yan sanda na Kanke.
Sanarwar ta ce nan take babban jami’in ofishin DPO ya tura tawagar masu binciken sirri, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma bin sawun waɗanda ke da alhakin aikata laifin.
A cewar ’yan sandan, samamen ya kai ga kama waɗanda ake zargi guda biyu da kuma ƙwato bindiga nau’in AK-47 ɗauke da harsasai masu rai guda
“A halin yanzu waɗanda ake zargi suna tsare a hannunmu, yayin da bincike ke ci gaba da gudana a sashen laifuka masu tsanani (VCRU) na rundunar domin kama sauran mambobin ƙungiyar masu laifin da kuma ƙwato sauran makamai da ke da alaƙa da laifin,” cewar wani ɓangare na sanarwar.
Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Filato (DCP), Usman Sheikh Adamu, ya yaba wa al’ummar yankin saboda sanya idon da suke yi da kuma ci gaba da ba ’yan sanda goyon baya.