An kama matashi kan zargin kashe matar ɗan uwansa mai juna biyu

0 1,046

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Kwara ta kama wani matashi mai shekaru 29, Sylvester Enemo, bisa zargin kashe matar ɗan uwansa mai juna biyu, Esther Enemo, a Ilorin.

An gano gawarta a bayan gidanta cikin daji tare da sassan jikinta da aka yayyanka, inda aka tsinci wasu a cikin buhu a ƙarƙashin gada, amma ba a ga kanta ba. Shaidu sun ce an ga wanda ake zargi da leda baƙa mai ɗauke da jini da safiyar ranar da aka kashe ta.

Kakakin ’yan sanda, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa an kama wanda ake zargi kuma an fara bincike domin tabbatar da adalci. Gawar marigayiyar an ajiye ta a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH).

Rundunar ta roƙi jama’a da su kwantar da hankali tare da guje wa yaɗa jita-jita da ka iya tayar da fitina.

Leave a Reply